9 Mayu 2026 - 09:17
Source: ABNA24
Gwagwarmaya Ta Sake Fasalin Yaƙin: Kan Kara Da Na Icce

Tseren tashe-tashen hankula na ƙaruwa a kudanci, a yanayin da ae samun sauyi a fili a yanayin fafatawa tsakanin Hizbullah da sojojin Isra'ila, waɗanda a halin yanzu ke fuskantar yanayin gajiyarwa mai girma, tare da koma baya a ikon hana yaɗuwar wutar yakin zuwa tsakiyar arewa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Abubuwan da ke faruwa a fagen fama a fagen Lebanon suna nuna wani sauyi mai inganci a yanayin fafatawa, domin yanzu ba a auna yaƙin da girman hare-haren da ake kaiwa juna kawai, sai da ikon gwagwarmaya na tilasta wani yanayi mai dogon gajiyarwa da kuma wargaza duk wata tabbatuwar maƙiyi a fagen daga. Sabanin wannan lamarin, muhawarori a kafafen yaɗa labarai da kuma cikin cibiyoyin soji da tsaro na Isra'ila, suna nuna wani matakin damuwa game da gazawar sojojinsu na shawo kan wannan salon yaƙin, musamman tare da amincewarsu cewa gwagwarmaya tana da tsarin sarrafa jirage marasa matuki cikin sauƙi da rarraba su wanda zai iya kiyaye yawan hare-haren, duk da ayyukan tashin bama-bamai da rugujewa.

Wannan yanayin bai tsaya kan fagen soji kai tsaye ba, har ma yana da alaƙa da sake tabbatar da daidaiton haɗin fagage wanda Tel Aviv da Washington suka yi ƙoƙarin shawo kansu. A wannan fanni, ƙididdigar Isra'ila da kanta tana nuna cewa Hizbullah bata ɗaukar fafatawa a matsayin wani fagen iyaka da ke a ware, sai dai ma tana daukaar ta a matsayin wani ɓangare na rikicin yanki mai fadi wanda a cikinsa ake haɗa lissafin Lebanon, Iran da Isra'ila a lokaci guda.

Dangane da haka, manazarcin harkokin soji a jaridar Ibrananci "Ma'ariv", Avi Ashkenazi, yana ɗaukar cewa ɗaya daga cikin manyan gazawa a tafiyar da yaƙi daga matakin siyasar Isra'ila shine barin Amurka ta haɗa tsagaita wuta da Iran da fagen Lebanon, yana mai ɗaukan cewa wannan haɗin ya bai wa Tehran "babbar kyauta" kuma ya tabbatar da daidaiton haɗin fagage.

A yayin da yake magana game da ayyukan fagen fama, Ashkenazi ya yi nuni da cewa lalata gadoji a kan kogin Litani bai cimma burin da ake so ba, yana mai bayyana hakan daga jami'an soji cewa ƙarancin ruwa yana ba da damar wucewar mayaƙa ba tare da buƙatar gadoji ba, wanda ke nuna barin hanyoyin samar da kayayyaki a buɗe ga Hizbullah. Ya na kuma ganin cewa Isra'ila a halin yanzu tana fafatawa da wani yaƙi na tsaron kariya mai iyaka a Lebanon ba tare da wani yunƙurin kai hari na gaske ba, yana mai gargadin cewa wannan salon yana ƙara yiwuwar samun hare-hare, a cewarsa.

Kuma a Isra'ila alamomi suna ƙaruwa kan zurfafa matsalar fagen fama da sojojinta ke fuskanta a kudancin Lebanon, tare da ƙaruwar tasirin jirage marasa matuki masu kai hari waɗanda Hizbullah ke amfani da su, kuma sun zama wani abin gajiyarwa na yau da kullun wanda ke tilasta gyare-gyare a jere a fagen sojoji da tsare-tsaren ayyukansu.

A wannan fanni, gidan talabijin na Ibrananci "Channel 12" ya ce ƙididdigar tsaro ta Isra'ila tana nuna cewa Hizbullah tana gudanar da wani tsari na musamman na sarrafa jirage marasa matuki a kudancin Lebanon wanda ya ƙunshi kusan mutane ɗari, suna aiki a cikin ƙananan ƙungiyoyi da ta rarraba, nesa da manyan runduna na gargajiya. Bisa ga ƙididdigar kanta, wannan tsari ya harba kusan jirage marasa matuki 160 zuwa ga sojojin mamaya, wanda kusan 90 daga cikinsu suna da alaƙa da wayoyi na fiber optic da ke haɗa su kai tsaye da masu sarrafa su.

Dangane da haka, ana ci gaba da samun "hare-haren tsaro" a fagen arewa na Falasdinu da aka mamaye, tare da ƙaruwar amfani da jirage marasa matuki masu kai hari, inda kafafen yaɗa labarai na Isra'ila suka ba da rahoton faruwar harew-hare biyu daban-daban a safiyar jiya, ɗaya a matsugunin Shlomi da kuma wani a yankin Ras al-Naqoura a yammacin Galili, wanda ya haifar da raunata mutuwar sojoji. A cikakken bayani, kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun yi magana game da fashewar abu da tashin hayaƙi a matsugunin Shlomi, kafin su tabbatar da cewa jirgi mara matuki ne ya kai hari a wani wuri a cikin matsugunin. A wani lamari na biyu, rahotanni sun yi nuni da fashewar wani jirgi mara matuki a yankin Ras al-Naqoura.

Kamar yadda gidan radiyon sojojin maƙiya ya ruwaito, sojoji biyu sun samu munanan raunuka da matsakaita sakamakon wani jirgi mara matuki mai fashewa da ya same su kai tsaye a Ras al-Naqoura kusa da iyakar Lebanon, yayin da wani soja kuma ya samu raunuka matsakaita a wani hari na biyu da jirage marasa matuki suka fashe kusa da rundunar Isra'ila a cikin kudancin Lebanon. Manazarcin gidan talabijin na "Channel 15" na Ibrananci yayin da yake sharhi kan wakio’in biyu ya ce Hizbullah "ta dawo ta yi duka ta hanyar jirage marassa matuki masu dauke da ababen fashewa a cikin yankin Isra'ila kuma ta haifar da rauni a cikin sojojin Isra'ila," wannan na nuni ne da ƙaruwar tasirin jirage marasa matuki masu kai hari wajen kai wa sojojin Isra'ila da wuraren tsaronsu na kan iyaka hari.

A daidai wannan lokaci, a matsayin ramuwa ga kai hare-haren da aka kai wa yankin kudancin birnin Beirut, da kuma tabbatar da daidaiton "Kan Kara Da Na Icce," Gwagwarmayar Lebonan ta kai wa sansanin Sharaga (hedikwatar gudanarwa na kwamandancin rundunar Golani da kuma wurin da rundunar Egoz take) da ke kudancin matsugunin Nahariya hari da wasu rokoki na musamman. Bayan harbin wuraren kai tsaye, an ji karar ƙararrawa a wani yanki mai faɗi na yammacin Galili, inda kafafen yaɗa labarai na Isra'ila suka ba da rahoton jin ƙararrawa a Nahariya da kewaye, kafin su bazu zuwa Akka da yankin Kiriyot da ke arewacin Haifa, wanda ke nuni da faɗaɗa fannin fagagen tsaro da soji a arewa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha